Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Imemc cewa, a jiywa wasu yahudawan sahyuniya sun mayar da wani masallaci mai dadaden tarihi a cikin yankunan Be’ir Shaba a matsayin wani wurin bude ido domin hana musulmi gudanar da salla.
Bayanin ya ci gaba da cewa akwa mabiya addinin muslunci da adadinsu yah aura dubu goma ayankin, a halin yanzu sun wayi gari basu da masallaci da za su rika gudanar sallolinsu na jam’I a yankin, tun bayan da yahudawan suka dauki wannan mataki
An gina masallacin ne dai tun shekara ta 1906, bayan da sahyuiyawa suka kori palastinawa fiye da 6000 daga yankin, sai yan sahyuniya suka mayar da wannan wuri mai tsarki zuwa wurin da suke shakatawa da tabarruji.
Bayan korari dubban palastinawa daga wannan wuri, yahudawan sahyuniya yan kaka gida sun ci gaba da yin hijira daga wasu yankuna suna dawowa wurin suna zama, inda gwamnatin sahyuniya ta ci gaba da gina matsugunnan yan share wuri zauna, wadanda suke ci gaba da mamaye yankin.
Yahudawan haramatacciyar kasar Isra’ila dai sun shahara wajen cin zarafin mabiya addinin muslunci palastinawa mazauna wadannan yankuna, amma dai kuma hakan bai sanya manyan kasashen duniya daukar matakan kare su ba.
2624868