Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-musalla bcewa, a jiya ne Ayatollah Sayyid Bashir Najafi da Ayatollah Muhammad said Hakim da kuma Ayatollah Fayyad daga cikin manyan malaman addinin muslunci a kasar Iraki suka bayyana cewa babban dalilin dakile bazuwar 'yan ta'addan daesh a Iraki da Syriashi ne tawassuli da ahlul bait iyalan gidan manzon Allah.
A wani rahoton kuma sojojin kasar Iraqi sun sami nasarar dawo da ikon gwamnatin kasar a garin amerli a arewacin kasar watanni biyu bayan da kungiyar yan ta’adda ta Da’esh ta karbe iko da shi.
Mai magana da yawun sojojin kasar ta Iraqi ya fadawa yan jaridu cewa bayan watanni biyu da mamayar garin na Amerli wanda ya ke kilomita dari da sabain daga birnin Bagdaza, mamaya na tsawon watanni biyu a yau lahadi sojojin kasar na Iraqi tare da goyon bayan mayakan masu sa kai na kasar.
Jim kadan bayan dawo da ikon gwamnatin kasar a garin amerli dai jami’an agaji sun fara shigo da kayakin agaji na gaggawa kamar abinci da magunguna ga mutanen da yan ta’addan suka yi garkuwa da su a yankin na lokaci mai tsawo.
Ministan matasa na kasar Iraqi Jassem Hamad da kuma priministan kasar mai barin kujera Nuri Al-Maliki duk sun taya mutanen garin murnin fita karkashin mamayar yan ta’ada.
A garin sulaimaniya na kasar ta Iraqi sojojin kasar suna ci gaba da korar dakarun kungiyar ta Daesh daga garin.
2625188