IQNA

An Kira Domin Dakile Yaduwar 'Yan Ta'addan Daesh A Cikin Kasar Canada

16:26 - December 24, 2014
Lambar Labari: 2625594
Bangaren kasa da kasa, Shahin Naz Sadighi shugabar cibiyar kula da ayyukan mulsunci ta kasar Canada ta yi kira ga mahukuntan kasar du zama cikin fadaka dangane da aikace-aikacen kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawabah Fito cewa, Shahin Naz Sadighi shugabar cibiyar kula da ayyukan mulsunci ta kasar Canada ta yi kira ga mahukuntan kasar du zama cikin fadaka dangane da ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh masu matukar hadari.
Musulmin kasar suna mayar da hankali matuka wajen tattauna lamurra da suka shafe su da kuma wadanda ska shafi duniyar musulmi, musamman ma  acikin wannan yanayi da ake kara samun bullar wasu kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi da ke kara tsananin adawa ga msuulmi mazauna wadannan kasashe na turai.
Bayanin ya kara da cewa musulmin Canada sun fara gudanar da babban taro ne a cikin shekara ta dubu biyu da uku domin kalu balantar abin da ake yadawa dangane da addinin musulunci bayan harin sha daya ga satuba na ta’addanci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasar.
Su dai musulmi dai dais u ne suka fi saurin karuwa  akasar Canada inda a halin yanzu su ne kashi uku cikin dari na dukkanin al’ummar kasar, wanda hakan ke nuna yadda suke samun ci gaba kuma adadinsu yake nikawa cikin kan kanin lokaci, sabanin sauran mabiya sauran addinai.
2625351

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha