Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Youm Sabi cewa, a jiya babbar cibiytar da ke sanya ido kan harkokin addinin muslunci a duniya an baiwa babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa na kasar Masar Shali Allam lambar yabo ta malamin da ya fi taka rawa wajen ganin tabbatar sulhu a duniya baki daya.
A jiya Sheikh Shuaki Allam babban malamin kasar Masar mai bayar da fatawa ya bayyana yan kungiyar ta’adda na daesh da cewa suna taka mummunar rawa wajen bakanta sunan addinin musuluci da bata manar ayoyin kur’ani mai tsarki da fasararsu ga sauran al’ummomin duniya.
Shehin malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar Sheikh Shauqi Al-allam ya bayyana cewa kungiyar gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya da bas u da wata alaka da addinin muslunci balantana koyarwarsa mai tsarki.
Wani bayani da ofishin da ke a cibiyar bayar da fatawa da yake jagoranta a birnin kahira ya fitar a jiya malamin ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Daga karshe ya yi Allawadai da kakkausar murya danmgane da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta daesh suke yi yanzu haka a cikin kasashen syria da iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma izidawa da kuma sauran bangarori na musulmin kasar.