IQNA

An Cafke wani Mutum Da Ya Keta Alfamar Masallaci A Calofornia

17:02 - December 28, 2014
Lambar Labari: 2643670
Bangaren kasa da kasa, an kame wani mutum wanda yak eta alfarmar wani masallaci mallakin mabiya addinin muslinci abirnin California na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, a cikin wannan mako ne aka kame wani mutum wanda yak eta alfarmar wani masallaci mallakin mabiya addinin muslinci abirnin California na kasar Amurka domin ladabtar da shi kan aikinsa.
A wani rahoto kuma jami’an tsaron Amurka sun kashe wani matashi da su ka zarga da kai musu hari da adda. Tashar Telbijin din ta kasar Amurkan ta ce an kashe matashin dan shekaru sha bakawai  ne mai suna Humboldt Adam Jager.
Majiyar ‘yansadan Jahar Carlifonia ta ce ta ce matashin ya kai hari ne da adda akan jami’an ‘yan sanda da su ke kan babbar hanya da ke tsakanin Carlifoia da kuma Hoopa.
Kisan na bayan na ya afku ne dai adaidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama su ke zargin jami’an tsaron Amurka da amfani da karfin da ya wuce haddi akan fararen hula.
A makon da ya shude ma dai an yi gagarumar Zanga-zanga a birnin Newyork domin nuna kin amicewa da wankiyar da wata kotun kasar ta yi wa ‘yan sanda na kasashe bakaken fata biyu da ba su da makamai.
Wannan yana daga cikin irin abubuwan da ake kokawa da su kan matasalar nuna banbanci ga mabiya addinai marassa rinjaye da kuma bakaken fata a kasar Amurka a mussaman ma  awannan jaha.
2640403

Abubuwan Da Ya Shafa: california
captcha