IQNA

Kame Sheikh Ali Salman Cin Fuska Ne Ga Dukkanin Masu Neman ‘Yanci A Bahrain

16:44 - December 30, 2014
Lambar Labari: 2653551
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ta fitar da bayani da ke bayyana kamun da masarautar Bahrain ta yi shugaban jam’iyyar Wifagh Sheik Ali salman da cewa cin fuska ne ga dukkanin amsu gwagwarmaya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-manar cewa, kungiyar Hizbullah ta fitar da bayani da ke bayyana kamun da masarautar Bahrain ta yi shugaban jam’iyyar Wifagh Sheik Ali salman da cewa cin fuska ne ga dukkanin masu gwagwarmaya a kasar ta Bahrain da al’ummarta ke fuskantar zalunci.
Alkalin alkalai, kuma shugaban ma’aikatar sharia a nan Jumhuriyar Musulunci ta ne ya bayana irin wannan matsaya a jawabin da ya gabatar a gaban jami’an ma’aikatar sharia a ranar kare hakkin bil’adam ta duniya, wato ranar Laraba  goma ga watan decemban ta ta gabata.
Malamin ya kuma kara da cewa, akwai abin ban mamaki kwarai, ga wasu kasashen yamma, wadanda suke da mummunan tarihi na mulkin mallaka, na tsawon karnuka, da kuma satar arzikin wasu al-ummu a duniya.
Banda haka wasu daga cikinsu, a halin da ake ciki, suna mamaye da wasu kasashen duniya, ko kuma suna kissan mutane a wasu kasashe amma kuma su ne da bu de baki suna zargin wasu kasashe daban da take hakkin bil’adama a duniya.
Ya kuma yi suka kan irin tsarin kare hakkin bil’adama na wadanan kasashe, wanda ya hada da nuna fuska biyu a tsarin nasu, ta yadda misali a kasar Bahrain, fiye da shekaru biyu da suka gabata, mutanen kasar su ka fara yunkuri na samun damar ba da ra’ayisu a cikin harkokin gudanarwa a kasar su, amma wadan nan kasashe masu riya kare hakkin bil’adama, sun ci gaba da goyon bayan sarakunan kasar ta Bahrain wajen murkushe mutanensu.
Ganin cewa sauya shugabanci a kasar Bahrai zai cutar da mummunar manufofinsu a kasar da ma yanking aba daya.
2652214

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha