Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ya yi da Muhammad Kaid Divid wanda ya wakilci kasar Afirka ta kudu a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta daliban jami’a da ake gudanarwa yanzu haka ya bayyana cewa halartar wannan gasa da matasan suke na nuna hadin kai tsakanin matasa da al’ummar musulmi.
Wannan na daga cikin gasar da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa a jamhuriyar musulunci da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya, wanda a wannan karon ma an samu halartar wasu daga kasashe daban-daban da suka hada da nahiyar turai.
Daya daga cikin abubuwan da wannan gasa ta kebanta da su dai su ne bayar da muhimmanci ga kyautata karatu domin ya zama matashiya ga sauran makaranta, tare da samar da salon a karatu da harda a lokacin gasa, wanda shi ne irinsa bna farko, duk da nufin karfafa harkokin karatu da hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin matasa na kasashen musulmi.
Gasar dai ta banbanta dasauran, musamman ma ganin cewa dukkanin mahalrtanta daliban jami’oi ne a cikin kasashn musulmi na duniya, daga karshe kuma ana bayar da kyautuka na musamman ne ga wadanda suka fi nuna kwazo, sai kuma kyautuka na baki daya ga duk wanda ya halarci gasar.
2665224