IQNA

Kungiyar Kasashen Msulmi Zata Bude Ofishinta A Afirka Ta Tsakiya

22:20 - January 14, 2015
Lambar Labari: 2709754
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi za ta bude ofishinta abirnin Bangui fadar mulkin kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya da nufin gudanar da ayyuka na musamman a bangaren jin kai.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a byunkurinta na gudanar da ayyuka na musamman a bangaren jin kai kungiyar kasashen musulmi za ta bude ofishinta  abirnin Bangui fadar mulkin kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya bukaci da a dakatar da batun kafa sabuwar gwamnati a kasar sakamakon rashin samun daidaiton baki tsakanin bangarorin siyasar kasar kan wannan batu, ya bayyana cewa, tun bayan da shugabar rikon kwaryar kasar ta ayyana Muhammad Kamun a matsayin sabon Firayi minista tare da umartar shi da ya kafa sabuwar gwamnati, har inda yau take ba a samu daidaiton baki tsakanin bangarorin siyasar kasar ba,  inda 'yan Seleka suka nuna rashin amincewarsu da hakan.

Muhammad Kamun dai ya kasance na hannun damar  Jutodia wanda suka dora kan mulki bayan kifar da bozeze, inda ya rike matsayin ministan tattalin arziki a cikin gwamnatin Jutodia a ranar ashirin da uku ga watan yulin da ya gabata ne dai bangarorin da ke rikici a Afirka ta tsakiya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu.

Babbar manufar bude wannan ofishi dai it ace gudanar da ayyuka na taimako da kuma tabbatar da sulhu a tsakanin mutanen kasar wadanda suke rikici da juna, rikicin da yake da nasaba da banbancin akida.
2708663

Abubuwan Da Ya Shafa: Bangui
captcha