IQNA

Wakilin Iran Ya Zo A Matsayi Na 4 A Gasar Karatun Kur’ani Ta Duniya A Sudan

10:51 - January 15, 2015
Lambar Labari: 2709787
Bangaren kasa da kasa, wanda ya wakilci Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a dakin taro na Al-sadagha a birnin kahtum fadar mulkin kasar Sudan Mohammad Nourouzi shi ne ya zo a matsayi na hudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nailain cewa, mutumin da ya wakilci Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a kasar Sudan a cikin wannan mako Mohammad Nourouzi  shi ne ya samu matsayi na 4 a wannan gasa.
Ya bayyana cewa gudanar da gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa ya bayyana cewa gudanar da irin gasa yana da matukar muhimmanci wajen kara hada kan al’ummar musulmi na duniya baki daya kamar dai yadda yake faruwa, tare da tababtar da cewa wannan alumma guda day ace kuma kur’ani mai tsarki shi ne littafin da ya hada ta.
Ita dai wannan na daga cikin gasar da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa a jamhuriyar Sudan da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya, wanda a wannan karon ma an samu halartar wasu daga kasashe daban-daban da suka hada da nahiyar turai baki daya.
Ko shakka  babu daya daga cikin abubuwan da wannan gasa ta kebanta da su dai su ne bayar da muhimmanci ga kyautata karatu domin ya zama matashiya ga sauran makaranta, tare da samar da salon a karatu da harda a lokacin gasa, wanda shi ne irinsa bna farko, duk da nufin karfafa harkokin karatu da hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin matasa na kasashen musulmin duniya.
Gami da cewa gasar dai ta banbanta dasauran, musamman ma ganin cewa dukkanin mahalrtanta daliban jami’oi ne a cikin kasashen musulmi na duniya, daga karshe kuma ana bayar da kyautuka na musamman ne ga wadanda suka fi nuna kwazo, sai kuma kyautuka na baki daya ga duk wanda ya halarta.
2707445

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gasa
captcha