IQNA

An Samu Raguwar Masu Mayar Da Hankali Ga Kin Jinin Musulunci A Jamus

22:57 - January 21, 2015
Lambar Labari: 2742220
Bangaren kasa da kasa, ana samun ci gaba ta fuskar rashin kulawa da masu kyamar musulunci a Jamus ta yadda a yanzu ba a kulawa da su sosai kuma abin da suke yana rasa tasiri.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, masu kyamar musulunci a Jamus suna ci gba da abin da ske yi ta yadda a yanzu ba a kulawa da su kamar lokutan baya.
Sa’ilin da ake kai farmaki kan masallatai da cibiyoyin addinin musulunci da kan mata masu saka hijabi a Faransa da wasu kasashen turai bayan kai harin birnin pari fiye da mutane dubu talatin da biyar sun gudanar da zanga-zanga a jiya a kasar Jamus domin nuna rashin amincewarsu da tsangwamar da ake nuna ma musulmi a cikin kasashen turai musamman ma a kasar ta Jamus.
Mataki da mahukuntan kasar ta Jamus suka dauka na nuna rashin amincewa da duk wani mataki na takura mabiya addinin muslunci ya harzuka masu tsatsauran ra’ayin kiyayya da musulmi, da ke neman a kori duk wani musulmi daga kasar, bisa hujjar cewa akasarin musulmin kasar baki ne.
Shekaru hudu da suka gaba gabata, shugabar gwamnatin jamus ta fadi irin wannan magana, tare da bayyana cewa a kowane lokaci mabiya addinin muslunbci suna iko da ‘yancin da su gudanar da harkokin addininsu a kasar Jamus kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yarje musu.
2736657

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha