
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Russia Today cewa, a jawabinsa na jiya shugaban kasar Amurka Barak Obama ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da da abin da ya kira nuna kiyayya ga yahudawa sai kuma cin zarafin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a cikin wasu kasashen turai.
A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa na jiya a gaban majalisar dokokin kasar ta Amurka, bayanin ya mayar da hankali kana bin ake kira tozarta yahudawa da kuma nuna musu kyama, duk kuwa da cewa yay i kokari ya nuna damuwarsa kana bin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a cikin wasu kasashen ymmacin turai na cin mutunci.
Shugaban na Amurka y ace babu wani dalili da wani bangare zai tsani wani bangare, dmin kuwa a cewarsa a halin yanzu dukkanin duniya ta zama bu guda uma ana bukatar hadin kai tsakanin dukkanin al’ummomi domin tunkarar barazanar ta’addanci wadda ba ta bar kowa ba kamar dai yaddad ya fada a cikin wannan jawabi nasa.
Haka nan kuma ya bukaci da a daina azuzuta wutar riki ta hanyar yin bayanai masu kushi da kuma sosa zuciya, matukar ana bukatar zaman lafiya a tsakanin dukkanin al’ummu.
2739932