IQNA

Pop Francis Ya Bayyana Wajabcin Tattaunawa Da Mabiya Addinin Musulunci

21:50 - January 26, 2015
Lambar Labari: 2767850
Bangaren kasa da kasa, babban jagoran mabiya addinin kirista mabiya darikar Katholika Pop Francis ya bayyana muhimmancin da ke tattare da tattaunawa tsakanin addinin kirista da bangarorin addinai da hakan ya hada da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kafanin dillancin labaran kasar Faransa cewa, Pop ya bayyana wajabcin da ke tattare da tattaunawa tsakanin kiristanci da addinin muslunci domin hakan zai taimaka matuka wajen warware abubuwa da dama da suka kawo rashin fahimta.
Pop ya ci gaba da cewa a lokacin da yake zantawa tare da tawagar mahalarta taron tunawa da cika shekaru 50 da kafa cibiyar tattaunawa tsakanin addinin da wannan majami’a, wadda ta hada da wakilan musulmi da kuma na larabawa da suka zo daga kashe daban-daban da kuma wakilcin al’ummominsu.
Ya kara da cewa a lokutan baya bayan kafa kungiyar PISAI ana gudanar da irin wannan tattaunawa, amma sai yanzu ne aka kara gane muhimmancinta da kuma wajabcinta, domin ta hakan ne za a warware batutuwa da daman a rashin fahimta  atsakanin mabiya addinan biyu na muslunci da kuma kiristanci.
Pop Francin y ace babu wani zamani da ya zama dole  akan dukkanin shugabannin mabiya addinain biyu su zauna domin dakile duk wani shishigi da rashin fahimta a tsakain mabiyansu kamar wannan lokaci.
2763290

Abubuwan Da Ya Shafa: pop
captcha