IQNA

Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi Aiki Ne Na Kasashen Musulmi Da Na Yamma

23:12 - January 26, 2015
Lambar Labari: 2767853
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa aiki ne da ya rataya kan kasashen musulmi da na yammacin turai da su mike domin yaki da tsatsauran ra’ayi da ke jawo ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-misriyyun cewa, Badar Abdul-ati kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar a lokacin taron kasashen da ke yaki da Desh a birnin London ya bayyana cewa aiki ne da ya rataya kan kasashen musulmi da na yammacin turai da su mike domin yaki da tsatsauran ra’ayi wanda a halin yanzu dukkanin kasashe ke fama da shi.
Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da matsalolin da ake fama da su, manyan cibiyoyi irin darul Ifta da kuma cibiyar ilimi ta Azahar za su taka gagarumar rawa wajen fitar da wasu hanyoyi na wayar da kan al’umma, musamman ma dai matasa daga cikinsu wadanda ake wanke wa kwakwale ana saka su hanyoyi na tsatsauran ra’yi da ta’addanci kamar dai yadda duniya take shedawa.
A ranakun alhamis da Juma’a ne gwamnatin Birtaniya ta dauki nauyin shirya zaman taro na kasa da kasa, dangane da batun yaki da ta’addanci da kasashen yammacin turai suke raya cewa suna yi, amma kuma dukkanin abin tataunawa a taron bai wuce batun yaki da daesh ba, wanda har yanzu dukkanin kasashen da suke raya cewa suna yaki da sub a su iya tabuka komai ba wajen murkushe yayan kungiyar.
Kasashen musulmi da suke fama da wannan balai ne dai suke yin iyakacin kokarinsu tare da abokansu na gaskiya domin kare kansu da kasarsu da kuma al’ummarsu daga sharrin yan ta’adda masu kafirta musulmi.
2761094

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha