IQNA

Ayyukan Daesh Sun Yi Hannun Riga Da Musulunci Kuma Sun Kama Da Khawarej

17:00 - February 02, 2015
Lambar Labari: 2798518
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta bayayyana ayyukan ta’addancin da kungiyar ISIS ke gudanar da cewa ba su da wata alaka da addinin muslunci suna ma bata sunansa ne a idon duniya.

Kamfani dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-sharq cewa babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa kungiyar da ake kira ISIS gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya.  
Kamar yadda ya zo a cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar Darul Ifta a birnin Alkahira ya fitar a jiya Talata, Sheikh Al-allam ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta ISIS suke yi yanzu ahak a cikin kasashen Syria da Iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma zidawa da kuma sauran bangarori na musulmi.
A Wani labarin kuma na daban rundunar sojin kasar Masar ta sanar da kasha uku daga cikin manyan jagororin kungiyar Ansar Bait Maqdis a wani farmaki da dakarun kasar suka kai kan maboyar 'ya'yan kungiyar a yankin Sinai, tare da kame wasu.
Majiyar rundunar sojin ta kasar Masar ta a Harin da sojojin suka kai a daren jiya a yankunan da 'yan ta'adda suka kafa tungarsu a cikin yankin Sinai, sun hallaka Fathi Auda, daya daga cikin manyan jagororin kungiyar da ke kaddamar da hare-haren bama-bamai a cikin kasar Masar, wadda a cikin makon nan ta ISIS. sanar da yin mubaya'a ga kungiyar 'yan ta'addan.
a  cikin kasa da sa'oi arba’in da takwas da suka gabata Dakarun kasar Masar sun hallaka 'yan bindigar fiye da goma, an kuma cafke wasu masu tarin yawa, da suka hada da wasu 'yan kasashen ketare.
2798458

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha