IQNA

Kimanin Mutane Dubu 100 Daga nahiyar Turai Suka Hadewa Da Daesh

21:15 - February 08, 2015
Lambar Labari: 2824837
Bnagaren kasa da kasa, kimanin mutane dubu 100 ake sa ran suna hadewa da kungiyar ta’addanci ta Daesh a kasashen Syria da Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sudinfo.be cewa, a cikin wadannan shekaru mutane daga turai da dama ne suke hadewa da yan ta’adda kamar yadda bayanai masu tabbaci suka yi nuni da hakan.
Bayanan da jaridar kasar Spain ta bayar sun cewa mutane daga nahiyar turai tsakanin dubu 30 zuwa 100 suka hade da daesha  cikin a kasashen na Iraki da Syria domin yaki tare da taimakon wasu daga cikin kasashen yankin, inda suka fita ta hanyoyin Marakesh da kuma Spain zuwa Syria kamar yada jaridar ta fada.
Kafofin yada labarai da dama na kasar Iraki sun bayar da rahoton cewa jiragen yakin Amurka sun jefa wasu akwatuna shakara da makamai ga mayakan kungiyar 'yan ta'adda na ISIS a arewacin kasar Iraki. 

Wannan lamari dai yana faruwa ne a daidai lokacin da Amurka take jagorantar wani kawance da ya hada da abokanta turawa, da kuma 'yan koranta daga cikin kasashen larabawa, da suka hada da Saudiyya, Qatar da kuma Jordan, domin abin da suka kira yaki da kungiyar ta ISIS a  cikin kasashen Iraki da Syria.

Al'ummomin kasashen na Iraki da Syria na cewa kawancen wadannan kasashe da sunan yaki da ISIS tsabar karya ce da munafunci kawai, domin dukkanin kasashen da ke gaba-gaba a cikin kawancen su ne suka kafa ISIS kuma suke taimakonsu, kamar yadda aka ga jiragen yakin Amurka na safke wa 'yan ISIS da tarin makamai a yankuna daban-daban na Iraki.

2823754

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha