IQNA

Za Bude Wata Cibiyar Tattaunawa Tsakanin Addinai A Masar

19:44 - February 09, 2015
Lambar Labari: 2829312
Bangaren kasa da kasa, za a bude wata bababr cibiya domin tattaunawa tsakanin mabiya addinai karkashin Sheikh Ahmad Tayyib musamman addininan muslunci da kiristanci a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, a Masar ana shirin za a bude wata bababr cibiya domin tattaunawa tsakanin mabiya addinai musamman addininan muslunci da kiristanci a kasar.

Daga cikin malaman da za su kula da shirin Sami Muhammad Nur malamin harshen Faransanci da tarjamar Azhar, Kamal Buraika Abdulsalam, malamin harshen turanci a jami'ar, sai kuma Rida Muhammad Dakik na jami'ar Tanta malamin Falsafa da usul, sai kuma Muhammad sulaimani mai bincike kan harkokin tattaunawa a tsakanmin addinai.

A nasa bangare jagoran mabiya darikar katolika fafaroma ya yi kira ga chochi ta ci gaba da yunkurin na tattaunawar fahimtar juna da sauran addinai musamman addinin musulunci, ya kuma ce, yin tattaunawa da musulmi yana da muhimmanci sosai wajen wanzar da zaman lafiya.

Da yake jawabi ga jakadu a fadar, ya bukaci cocin ya yi wa'azantarwa ga wadanda basu bada gaskiya ba domin yakar abin da ya kira mutuwar zuci da koma bayan tarbiyya a wannan zamani ,Ya kuma yi kira da a sabunta yunkuri wajen yaki da talauci da kuma kare muhallia douk fadin fadin duniya. 

Kasar Masar dai na taka gagagrumar rawa wajen ganin an samu daidaito na fahimta tsakanin mabiya addinai da aka safkar daga sama, musamamn kiristanci da muslunci.

2826913

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha