
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin mayna malaman addinin muslunci a kasar Lebanon Allamah sayyid Ali Fadlullah ya yi Allawadai da kakausar murya dangane kisan kibdawa Misrawa 21 da yan Daesh suka yi a kasar Libya tare da bayyana cewa, hankoron masu aikata ta'addanci shi ne haddasa fitina tsakanin mabiya addinan kuristan da na muslunci.
Malamin ya ci gaba da cewa akwai makiya dukaknin addinai biyu wadanda suke ta hankoron ganin sun haifar da baraka mai tsanani a tsakaninsu, kuma irin yadda mabiyan addinain biyu suka yi tsayin daka wajen ganin ba a hada su fada babban abin yabo matuka.
Ya ci abin day an ta'adda ISIS ke yi ko shakka babu suna yi makiya muslunci hidima ne ko suna ko kuma ba son haka, balantana abu ne zahiri ne suna sane bil hasali ma bakin su daya, shirinsu daya domin rarraba musulmi da haifar da rikici tsakaninsu da kiristoci da bata sunan a dinin a idon duniya.