Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nujoom Misr cewa, a yau ne aka gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal wadda ake gudanarwa tare da hadin gwiwa tsakanin cibiyar yada al’adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO da aka fara tun 2013 zuwa 2015, da kuma bababr cibiyar yadawa da kuma da harkokin musulunci ta birnin Dakar.
Mahalarta wannan gasa dai sun kai mutane 120, da suka fara karawa da junasu a dukaknin bangarorin gasar, wadda ta hada hardar kur’ani mai tsarki daga farko zuwa karshe, sa kuma bangaren kyautata karatun kur’ani ko kuma tawidi, bayan nan kuma akwai amsa tambayoyi na tafsirin ayoyin kur’ani mai tsarki bai daya.
Za a kamamla wannan gasa a birnin na Dakar bababn birnin kasar Senegal, inda za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a gasar, kuma bayar da kyautuka na baki daya ga dukaknin mahalarta, sai kuma ga wadanda suka lashe a matakai na daya zuwa na uku.
2876826