IQNA

23:04 - February 21, 2015
Lambar Labari: 2879246

Kakkausar Suka A kan Obama Saboda Kalaman Da Ke Nuna Goyon Bayan Musulunci

Bangaren kasa da kasa, bayan kalaman da sugaban kasar Amurka ya yin a nuna cewa yan ta’adda bas u wakiltar addinin muslunci da musulmi hakan ya sanya shi yana san suka daga masu tsatsauran ra’ayi a fadar white house.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar New York Post cewa, Obama yana sha gagarumar suka daga masu tsananin kiyayya da muslunci a fadarsa, saboda abin da suka ce nuna alamun goyon bayan addinin muslunci da yake yi.
Barack Obama shugaban Kasar Amurka ya furta cewa Amurka  ko kadan ba ta yaki da Musulunci a matsayinsa na addini. Shugaban na kasar Amurka ya bayyana haka ne a yayin da ya ke gabatar da jawabi a gaban wakilan kasashe sattin da su ke halartar taron ‘yaki da ta’addanci, da aka bude a birnin Washington.
Ya ce dukkanin wadanda su ke yaki a karkashin kungiyar Isil, ‘yan ta’adda ne kuma wajibi ne duniya ta yi fada da tushen abinda ya ke maida mutane zama masu wuce gona da iri.
Har ila yau shugaban na Amurka ya bayyana cewa; Yarda da cewa alka’ida da Isil ko Da’ish, suna da alaka da addinin Musulunci, tamakar amincewa ne da parpagandar da su ke yi. 
Wannan ba shi ne karon farko ba da shugaban na Amurka ya ke yin maganganun da su ke nuni da mika hannun kawance ga addinin Musulunci.
A shekarar dubu biyu da tara a fadar mulkin kasar masar ya yi magana kwatankwacin wannan, haka nan kuma a yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na bayan nan.
Sai dai a kasa, siyasar gwamnatin Amurka ba ta tafiya kafada da kafada da abinda shugaban kasar wanda mahaifinsa musulmi ne ya ke fada. Matsalar Amurka da al’ummar musulmi, ta rigayi zaman Barrack Obama shugaban kasa.
A bisa abinda aka tsara shi ne cewa wadannan kungiyoyin za su zama masu yi wa manufofin Amurka aiki, sai dai daga lokacin da za su fita daga karkashin ikonsu, sai su ka maida hankali wajen bakanta sunan addinin Musulunci a idon duniya.
A cikin shekaru ashirin na bayan nan, yaduwar ayyukan ta’addanci da masu shi, ke fakew ada sunan Musulunci, sannan kuma a lokaci daya da abinda kasashen turai su key i na fada da addyukan ta’addancin, sun jefa kasashen musulmi cikin matsananciyar wahala.
2876859

Abubuwan Da Ya Shafa: Obama
captcha