IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Suka Kan Harin Yahudawa Kan masallaci Da Majami’a

23:30 - March 01, 2015
Lambar Labari: 2915455
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakakusar suka da yin Allawadai dangane da harin ta’addancin da yahudawan sahyuniya suka kai a yammacin garin Bait Laham da ke cikin palastinu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a jiya ne kungiyar kasashen musulmi ta fitar da bayani da ke yin kakakusar suka da yin Allawadai dangane da harin ta’addancin da yahudawan sahyuniya suka kai a yammacin garin Bait Laham a cikin palastinu inda suka kone su kurmus.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki dai wanda ba shi ne na farko ba kuma ba zai zaman a karshe ba, ya zo ne a lokacin da yahudawan masu tsattsauran ra’ayi suke ci gaba da zafafa hare-harensu babu kakkautawa a kan palastinawa musulmi da kuma mabiya addinin kirista ba tare da wani banbanci a tsakaninsu ba.
Wadannan yahudawan Isra’ila dai suna aikata hakan tare da cikakken goyon bayan haramatacciyar gwamnatinsu, da ke basu kariya a kowane lokaci suke aikata irin wannan barna da ta’asa kan palastinawa de aba su da kowa sai Allah.
Haka nan kuma bayanin kungiyar ya soki kasashen da suke raya cewa suna kare hakkokin bil adama  akasashen turai su ne kan gaba wajen mara baya ga irin wadannan ayyuka na ta’addancin Isra’ila kan sauran al’ummomi masu rauni, ya ce dole a dauki dukkanin matakai domin takawa irin wadannan bakaken ayyuka birki na cin zalun.
Wannan lamari dai ya ja hankulan al’ummoin duniya dangane da irin tabargazar da yahudawan sahyuniya suke aikatawa kan al’ummomin duniya, inda hakan bai takaita ga musulmi da wuraren ibadarsu ba, har ma a kan mabiya addinin kirista da ke yankunan da suka mamaye.
2913067

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi
captcha