Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na world Bulletin cewa cibiyar Almizan ta kare hakkin dan adam ta fitar da cikakun bayanai dangane da halin da palastinawa mata suke ciki sakamkon halin da aka jefa na zaluncin yahudawa.
Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta shigo sahun sauran cibiyoyin kasa da kasa wajen sanar da cewa haramtacciyar kasar Isra’ial ta tafka laifuffukan yaki a kan Palastinawa a yakin baya-bayan nan da ta kaddamar kan al’ummar Gaza.
A sabon rahoton da ta fitar a yau din nan Laraba, kungiyar ta ce daga dukkanin alamu da gangan sojojin HKI suke kai hari kan fararen hula da cibiyoyinsu, wanda hakan yana a matsayin laifin yaki ne.
Kungiyar ta ce ta gudanar da bincike kan hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai Gazan da suke tabbatar musu da cewa sun kai harin ne da gangan kan fararen hula ba tare da wani jan kunne ba.
Daga karshe dai kungiyar ta bukaci da a kai wannan batu nay akin Gaza kotun kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuffukan yaki don gudanar da bincike bisa gazawar da gwamnatin da kuma gwamnatin cin gashin kan Palastinawa suka yi wajen gudanar da bincike na hakika kan zargin laifuffukan yakin da ake zargin bangarori biyun sun tafka yayin yakin.