IQNA

Wajabcin Amsa Shubhohin ‘Yan takfiriyyah Domin Kada A Bata Sunan Musulunci

21:34 - March 11, 2015
Lambar Labari: 2966327
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam bababn malami mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana wajabcin amsa irin shubhohin da masu akidar kafirta muslmi suke dauke da su domin kare musulunci daga gurbata.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Shauki Allam a lokacin da yake ganawa da Ahmad Wuld Ahl Dawud minister mai kula da harkokin muslunci a kasar Mauritania ya bayyana cew, wajibi ne a amsa irin shubhohin da masu akidar kafirta muslmi suke dauke da su domin kare musulunci daga gurbata da kuma jya manufarsa ta shiryar da dan adam.
Bayanin ya ci gaba da cewa ministan kasar Mauritaniya yana gudanar da ziyarar aiki ne a kasar masar domin yin bahasi dangane da muhimman batutuwa da suka shafi musulmin yankin, da kuma sanin hanyoyin da za a bi domin kara wayar da kan matasa da ake yaudara suna shiga wasu kungoyin yan ta’adda da sunan addini.
Babban mai bayar da fatawar na masar y ace aikin malamai su mike domin tabbatar da cewa sun sa al’umma kan sahihin tafarki, domin kuwa jahilci na datyya daga cikin abubuwan da suka a kan gaba wajen cutar da matasa, kamar su kansu masu cusa musu irin wannan tunai ba ilimin ne ya ishe sub a.
Shauki Allam y ace yin haka yana daya daga cikin manyoyi na yaki da ta’addanci, domin kuwa ba ta hanyar makami ne kawai a ayaki ta’addanci ba, za a hada biyu ne na makamin da kuma na gyara tunani da ilmantarwa.
2956524

Abubuwan Da Ya Shafa: Allam
captcha