IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Sukar Yadda Isra’ila Ke Cin Karenta Babu Babbaka

23:14 - March 16, 2015
Lambar Labari: 2996919
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen larabawa ta yi kakakusar suka dangane da yadda kasashen duniya suka yi shiru da bakunansu kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take cin Karen babu bababka akan palastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yau kungiyar kasashen larabawa ta yi kakakusar suka dangane da yadda kasashen duniya suka yi shiru da bakunansu kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take cin Karen babu bababka a kan al’ummar palastinu marassa kariya.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun sheakrun da suka gabata aka gabatar da daftarin kudirin neman amincewa da kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta, amma wasu kasashe suka ki amincewa da hakan, duk kwa da cewa su ne kan gaba wajen batun tattaunawar sulhu da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da palasinawa.
Daga cikin watan Fabriaru 5 gare shi zuwa 9 ga watan Maris, haraktacciyar kasar Yahudawan ta kame daruruwan palastinawa da sunan yunkurin tabbatar da tsaro, amma babu daya daga cikin kasashen ke babatun kare hakkin palastinmawa da ta kalubalanci wannan mataki.
Yanzu haka akwai palastinawa 6500 da suke tsare a gidajen Kason haramatacciyar kasar Isra’aila acikin gidajen kaso fiye da 22 a ssa daban-daban na yankin palastinu da aka mamaye.
2993816

Abubuwan Da Ya Shafa: larabawa
captcha