IQNA

An Lalata Mafi Yawan Masallatan kasar Afirka Ta Tsakiya Sakamakon Rikicin Kasar

22:54 - March 18, 2015
Lambar Labari: 3009666
Bangaren kasa da kasa, sakamakon rikicin da ya faru a jamhuriyar Afirka ta tsakiya akasarin masallatan kasar an rusa su ko kuma an yi musu barna

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na tashar PressTV cewa, rikicin da ya faru a jamhuriyar Afirka ta tsakiya yayi sanadiyyar akasarin masallatan kasar an rusa su ko kuma an lalata su, ta yadda kimanin masallatai 436 an rusa 417 a sassa daban-daban na kasar.
A nasa bangaren firayi ministan Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen aiwatar da shirin da gwamnatinsa ta sanya a gaba na dawo da doka da oda a fadin kasar baki daya, tare da shiga kafar daya da duk wanda ya nemi kawo tarnaki ga wanann shiri. 
Firayi ministan na Afirka ta tsakiya Kamun ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da wani jawabi da gidajen talabijin na kasar suka watsa kai tsaye, inda ya ce tuni gwamnatinsa ta fara aiwatar da dukaknin shirye-shiryenta domin ganin kasar ta farfado daga matsalolin da ta shiga, da hakan ya hada da batun tsaro da kuma habbaka tattalin arziki.

A daren juma'ar da ta gabata ce dai wasu mayakan kungiyar kiristoci suka kai farmaki a wasu unguwanni na mabiya addinin muslunci a cikin birnin Bangui, inda ya sha alwashin kame dukkanin wadanda suke da hannu a cikin wannan lamari domin gurfanar da su a gaban kuliya.

3007496

Abubuwan Da Ya Shafa: CAR
captcha