Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-sharq ta kasar Qatar cewa, an bude wata cibiyar koyar da ilmomin kur’ani da addinin muslunci da suka hada da tarbiya a garin Ibdan na jahar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Adadin daliban da aka fara dauka domin su fara samun horo na karatun kur’ani mai tsarki da sauran ilmomin addini sun kai su 150, da nufin kara yawansu a nan gaba a lokacin da cibiyar zata kara bunkasa ayyukanta a wannan jahar da ma sauran jahohi na kasar.
Wanann dai na daga cikin ayyukan da cibiyoyin da ke gudanar da airin wadannan ayyuaka a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka da ma wasu daga cikin kasashen duniya, da nufin koyar da karatun kur’ani mai tsarki da sauran ilmomi na addinin muslunci ga musulmi da suke bukatar neman sani.
Kasar dai tana rawa a wannan bangare, duk kuwa da cewa wasu daga cikin kasashe suna kokawa kan rawar da take takawa a daya bangaren na mara baya ga auukan ta’addanci da kuma renon kungiyoyin ‘yan ta’adda a cikin kasashen, wadanda a halin yanzu suka zama babban balai ga musulmi da ma sauran al’ummomin duniya baki daya.
Ana dai fatan cewa wannan shiri zai amfanar da mutane da suke samun horon na karatun kur’ani da sauran ilmomumomin addinin muslunci a wannan sabuwar cibiya.