IQNA

Kungiyar Daesh Ta Dauki Alhakin Kai Harin Ta'addanci A Tunisia

20:06 - March 19, 2015
Lambar Labari: 3012741
Bangaren kasa da kasa, kungiyar 'yan ta'addan Daesh ta ce ita ce ke da alhakin kaddamar da harin da aka kai a dakin tarihin kasar Tunisia da ke kusa ginin majalisar dokokin kasar wanda ya lakume rayukan mutane 22 da jikkata wasu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-nahar ta kasar Lebanon cewa, yan ta'addan IS sun ce su ke da alhakin kaddamar da harin da aka kai kasar Tunisia wanda ya nufi daruruwan yan yawon bude na kasashen ketare.

Mahukunta da farko sun bayyana cewar mutane  17 daga cikinsu ‘yan yawan shakatawa ‘yan kasasshen waje,  ne suka rasa rayukansu kana wasu da dama kuma suka sami raunuka sakamakon harin ta’addancin da wasu ‘yan ta’addan suka kai gidan tarihin Bardo da ke babban birnin kasar Tunis a yau din nan.

Shugaban gwamnati na kasar ne ya fadi hakan a wata ganawa da  yayi da manema labarai jin kadan bayan kawo karshen harin da ‘yan ta’addan suka  kai gidan tarihin a yammacin yau inda ya ce, harin yayi sanadiyyar mutuwar ‘yan yawan shakatawa su sha bakwai da suka fito daga kasashen ketare kamar yadda kuma ya ce jami’an tsaron sun kashe ‘yan ta’addan biyu da suka garkuwa da  wasu mutane sannan jami’an tsaro kuma suna ci gaba da neman sauran ‘yan ta’addan.

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun shigo gidan ajiye kayan tarihin ne da kayan soji a daidai lokacin da aka ce sama da mutane dari biyu  suna wajen inda suka yi garkuwa da wasu daga cikinsu,  sai dai kuma tuni aka kwato su daga hannun ‘yan ta’addan bayan an kashe su.

Gidan ajiye kayayyakin tarihin Bardon shi ne babban wajen ajiye kayayyakin tarihi a kasar Tunusiya da ke janyo hankulan ‘yan yawon shakatawa da yawan gaske, to sai dai kuma kasantuwarsa kusa da majalisar dokokin kasar ne ya sanya wasu suke tunanin mai yiyuwa ‘yan ta’addan majalisar suke nufi kai wa harin.

3010675

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha