IQNA

Jam’iyyun Siayasa A Pakistan Ba Su Gamsu Da Bayar Da Taimako Ga Saudiyya Ba

23:53 - April 08, 2015
Lambar Labari: 3110943
Bangaren kasa da kasa, jam’iyyun siyasa da kungiyoyin muslunci da kunhiyar Imran Khan sun nuna rashin gamsuwarsu da hankoron da gwamantin Pakistan ken a neman aikewa da taimakon soji ga Saudiyya domin yaki da Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ERY cewa, yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun gudanar da zama domin tattauna batun aike wa taimakon soji ga kasar Saudiyya domin kasha al’ummar Yemen.
Bayanin ya ci gaba da cewa da dama daga cikin jam’iyyun siyasa da kungiyoyin addini sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki na mahukuntan kasar da ke nemn jefa su cikin wani rikici nasiyasa da bai shafw su ba, wanda kuma idan ta dawo lamarin ba zai yi musu dadi ba.
Firayi ministan kasar ta Pakistan Nawaz Sharif da kuma ministan tsaronsa Khawajah Asef sun dage a kan aiwatar da manufar iyayen gijinsu na Saudiyya na kaddamar da taimako ga mahkuntan na Al Saud domin kasha al’ummar kasar Yemen.
Amma duk da haka sun fuskantar turajiya, domin kuwa hatta fitaccen mai adawa Imran Khan ya bayyana hakan da cewa ba maslaha ce ga kasar ta Pakistan ba, domin kuwa abin da yake faruwa Magana ce ta siyasa da hankorocin cimma manufa daga bangaren masu kai harin, wand aba shi da alaka da Pakistan.
Yanzu haka kasashen larabawan yankin tekun fasha sun gabatar da kudiri ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin neman halascin abin da suke na laifukan yaki a Yemen, daftarin kudirin bai ambaci ko daya daga cikin ayyukan yaki da Saudiyya take aiwatarwa a kasar ta Yemen da sunan yaki da 'yan kungiyar huthi ba, haka nan kuma kuma ya bukaci da a halasta kai musu hari karkashin bangare na bakawai na kundin tsarin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.
Tare da tilasta su amincewa da shugaban kasar wanda ya tsere zuwa Saudiyyah, rash ta ce wannan daftarin kudirin dai babu adalci da daidaito a cikinsa, ku akwai son rai matuka daga bangaren da ya shirya shi.
3103236

Abubuwan Da Ya Shafa: pakistan
captcha