Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahfaq News cewa, Haidar Ibadi firayi ministan kasar Irakia wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin ya bayyana cewa, Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya nuna cikakken goyon bayansa ga kokarin da al’ummar kasar Iraki suke yi domin ganin an kori yan ta’addan ISIS baki daya daga kasar.
Haidar Ibadi ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da Ayatollah Sisatani a birnin Najaf, inda ya tattauna muhmman batutuwa da suka shafi kasar, da kuma jan aikin da ake na ganin ganin an kori yan ta’adda da ke samuin goyon baya daga kasashe ketare daga kasar ta Iraki baki daya.
Haidar Ibadi ya ce malaman addinin muslunci dake Najaf dukkaninsu na goyon bayan gwamnati da al’umma dangane da kokarin da suke na tsarkake kasarsu daga yan ta’adda, kamar yadda suke karfafa dukaknin bangarori da su goyi bayan wanann kokari na ganin bayan daesh.
Dangane da masu kokarin yin farfaganda ta karya dangane da masu sadaukantar da kansu wajen yanto yankunan Iraki daga yan ta’addan kwa, ya bayyana cewa hankoro ne na kashe gwiwarsu da kuma baiwa yan ta’addan damar ci gaba da mummunaikinsu.
Bayan halartar janazar marihayi Sayyim Muhammad Bahrul Ulum da kuma ganawa da babban malamin addinin na Iraki Ayatollah Sistani, Haidar Ibadi ya gana da wasu manyan malaman da suka hada har da Ayatollah Ozma Ishaq Al-Fayyad.
3121173