Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, ma'aikatar tsaron kasar Yemen ta tabbatar da kashe daya daga cikin yayan gidan sarautar kasar saudiyya kuma babban jami'in sojin kasar kan yakokinta da kasar Yemen.
Fiye da kashi casa'in dukkanin wuraren da jiragen yakin masarautar Saudiyya suka lalata ba su da wata alaka da kungiyar Alhuthi, bil hasali ma gidajen jama’a ne fararen hula da kaddarorin gwamnati, da suka hada da makarantu, asibitoci, masallatai, cibiyoyin wutar lantarki, gadoji, cibiyoyin iskar gas gami da kamfanoni da ke samar da kayayyakin bukatar rayuwa a kasar.
Wannan ya sanya da dama daga cikin ‘yan siyasa a kasar ta Yemen suna ganin cewa amincewa da wannan daftarin kudiri da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi, yana daya daga cikin abubuwan kunya da ya aikata da tarihi ba za su taba mantawa da su ba, domin kuwa ya halasta zubar da jinin fararen hula a kasar Yemen a fakaice, tare da cika ma wata kasa burinta na siyasa da ya saba wa dokokin kwamitin, ta hanyar yin amfani da sunan kwamitin.
Duk da cewa a halin yanzu masarautar Saudiyyah ta samu lasisi daga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wanda ke gudanar da harkokinsa daidai da abin da ya dace da mahangar siyasar turawa musamamn ma Amurka, amma kuma hakan ba zai ba ta damar cimma babban burinta na tilasta al’ummar kasar Yemen da karfin bindiga su zama ‘yan korenta ba.
Ko da kuwa ta rusa musu kasa, da kashe wani adadi na al’ummar kasar da koma wace irin hujja masarautar ta fake ita, domin kuwa tarihi shi ne babbar sheda kan hakan, ganin cewa tun bayan da turawa suka kafa masarautar Al Saud kuma suka dora wannan masarauta kan al’ummar hijaz da a halin yanzu ake kira da sunan wannan masarauta wato Saudiyya, wannan masarauta ta yi iyakacin kokarinta tare da taimakon turawan da suka kafata domin mamaye kasar ta Yemen tare da shimfida ikonta a kansu, amma hakan ta ci tura.
3152467