IQNA

Manzon Majalisar Dinkin Duniya Ya Gana Da Ayatollah Sistani A Iraki

23:47 - April 21, 2015
Lambar Labari: 3188673
Bangaren kasa da kasa, manzon majalisar dinkin duniya ya gana babban malamin addinin muslunci a kasar Iraki Ayatollah Sayyid Sistani domin bayyana masa maharsa kan batun tsaro a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyya News cewa, Yankovich manzon majalisar dinkin duniya ya gana babban malamin addinin muslunci a kasar Iraki Ayatollah Sayyid Sistani domin bayyana masa maharsa kan batun tsaro da kuma sauran batutuwa da suka shafi kasar a wanan lokaci.
Jami'in ya halarci hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf, inda ya bayyana cewa shi ne wiri na farko da ya fara ziyarta kafin ganawa da kowa a birnin, kafin daga bisani ya gana da bababn malamin.
Bayan kamamla ganawarsa da shi kuma ya gana da wasu daga cikin manyan malaman addinin musulunci na birnin, inda bayyana musu sakon babban sakataen majalisar dinkin duniya, dangane da goyon bayan da majalisar ke bayawrwa da kuma jinjina wa malamai kan gudunmawarsu wajen zaman lafiyar Iraki.
Y ace daga bisani zai isa wasu daga cikin wuraren da yake bukatar ganewa idansa abin da ya faru da kuma sanin abin da zai hada na bayanai ga babban sakataren majalisar kan ahalin da ake cikia  kasar.
3179048

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha