Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alakhabar ta kasar Lebanon cewa, Nahez Hatar wani mai sharhi kan harkokin da ke kai da komowa dan kasar Jordan ya sheda cewa, Daudiyya ta tsorata ne da Iran shi yasa ta kaddamar da hari, kuma ta sha kayi da jin kunya a harin nata.
A bangare guda kuma masarautar Saudiyyah ta sanar da kawo karshen yakin da ta kaddamar kan al'ummar Yemen, bayan kwashe kwanaki ashirin da bakwai a jere tana lugudan wuta kan al'ummar kasar babu kakkautawa, da sunan yaki da 'yan kungiyar huthi da kuma dawo da shugaban kasar da ya yi murabus kuma ya tsere daga kasar.
Saudiyyah ta ce ta cimma burinta a kan wannan yaki da ta kaddamar kan al'ummar kasar Yemen, domin kuwa a cewarta ta kawar da barazanar da take fuskanta daga 'yan kungiyar Huthi da kuma tsohon shugaban kasar, ta hanyar abin da ta kira rusa makamansu masu linzami.
Tun bayan kaddamar da harin na Saudiyyah a kan al'ummar kasar Yemen, al'ummomin duniya masu lamiri da kuma wasu daga cikin gwamnatocin kasashen duniya masu 'yancin siyasa, sun yi Allawadai da wannan mataki da masarautar ta Al Saud ta dauka kan na kashe mutanen kasar da ke makwabtaka da ita, ta hanyar yi musu ligudan wuta na kan mai uwa da wabi da sunan yaki da kungiyar huthi, inda a wasu kasashen an gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da da wadannan hare-hare kan Yemen.
Masana da dama suna ganin cewa batun dakatar da yakin ba hannun Saudiyyah yake ba, domin tun asali yakin ba nata ba ne, yaki ne na makiya musulunci take aiwatar musu, kuma hakan na daya daga cikin shirinsu na rusa kasashen musulmi da na larabawa, wanda kuma masarautar Al saud da turawan mulkin mallaka suka kafa tare da mika mata dukkanin madafun iko a kasar wahayi wadda turawan suka mayar Saudiyyah ta yanzu, ita ce babban makamin da suke amfani da shi a halin yanzu domin aiwatar da wannan shiri nasu na rusa kasashen musulmi da na larabawa, kama da irin rawar da masarautar ta taka wajen rusa kasashen.
A nasu bangaren kuma masana kan harkokin tsaro da ayyukan soji suna ganin cewa masarautar Al Saud ba ta iya cimma ko daya daga cikin manufofin kaddamar da yakin ba da ta shelanta tun daga farko, domin kuwa ba iya kawarda ko murkushe kungiyar huthi ba, haka nan kuma ba ta iya dawo da yaronta kan mulkin kasar ta Yemen ba, wanda halin yanzu ya tsere zuwa birnin riyad.
Sai dai kam ta samu gagarumar nasara wajen kashe fararen hula da dama da suka hada da mata da kananan yara da tsoffi, tare da mayar da daruruwan yara marayu, da kuma rusa cibiyoyin ilimi da masallatai, da gadojin da suka hada manyan biranan kasar, kamar yadda ta samu nasara wajen rusa cibiyoyin wutar lantarki da na iskar gas da kuma asibitoci, gami da dubban gidajen jama'a.
3190907