Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, daga jiya zuwa yau tare da barazanar da yan ta’addan suke yi wa masu gudanar ziyarar Iam Hadi (AS) a ranar shadarsa hakan bai hana masu ziyarar tafiya a kasa ba zuwa Samirra ba mai tsarki.
Tun kafin wannan lokacin dai duban daruruwan masu ziyara daga dukkanin sassa na kasar Iraki sun isa yankuna da ke kusa da hubbaren nasa mai tsarki, kuma daga bisani bayan karatowar lokacin shahar Imam Hadi (AS) sun nufi hbbaren nasa da ke garin Samirra.
Yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen da suka kafa su kuma suke daukar nauyinsu, sun yi iyakcin kokarinsu domin hana wannan aiki na ziyara da kuma tuwana da raranr shahadrsa, amma Imani da dogaro da Allah sun sanya nuna halin ko in kula da wannan barazana daga masu aikin ziyarar, duk da cewa a yankin akwai barazana ta tsaro.
Mahukuntan a kasar dai sun ce kimanin mutane miliyan uku ne suke halartar tarukan na tunawa da shahardar Imam hadi da suka fito daga dkkanin sassa na Iraki, kamar yadda kuma wasu sukazo daga kasashen ketare, an bayan da rahoton cewa wasu yan ta’adda sun kaddamar da hare-haren kunar bakin wake akn masu ziyara da suke komawa gida, wasunsu sun yi shahada.
3190953