Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Luis Math babban jami'in hukumar kare hakkokin bil adama ta majalisar dinkin duniya a kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya bayyana cewa akwai bukatar daukar matakai domin kare hakkokin musulmi a kasar da suke fuskantar barazana.
Akalla mutum daya ne ya rasa ransa a lokacin da wasu daruruwan mutane masu zanga-zanga suka kai farmaki kan wani sansanin dakarun majalisar dinkin duniya a arewacin jamhuriyar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
akakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ne ya sanar da hakan a daren jiya, inda ya bayyana cewa, mutanen da adadinsu ya kai zuwa sun nufi sansanin ne da ke yankin Kaga Banduru da ke tazarar kilo mita a arewacin Bangui, wasu daga cikinsu kuma suna dauke da adduna, wanda hakan ya tilasta jami'an na majalisar dinkin duniya yin amfani da karfi a kansu, inda mutun daya ya rasu wasu kuma suka samu raunuka
ya ce sun yi takaici matuka dangane da faruwar hakan, kuma tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin, da kuma jin korafin da al'ummar yankin suke da shi ga majalisar dinkin duniya.
3210124