Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBC cewa, Muhamamd Anwar daya daga cikin jagororin mabiya addinin muslunc a garin Windrose na kasar Canada ya bayyana cewa, sun fara bayar da horo ga musulmi domin sanin yadda za su kare addininsu.
Ya ci gaba da cewa an dauki wanann mataki bisa la'akari da yadda masu tsananin adawa da addinin muslunci suke ci gaba da kokarin ganin sun bata sunan wannan addini a kasar, ta hanayar bayyana shi a matsayin addinin ta'addanci da jahilci da dabbanci, suna masu kafa dalili da ayyuakan wasu jahilan musulmi masu ta'addanci da sunan muslunci a wasu kasashe.
Mabiya addinin muslunci an fuskantar matsaloli a kasar daga masu tsananin kiyayya da musulunci musamman a birnin na Wildrose, inda a cikin 'yan lokutan da suka gaba an kai hari kan musulmi tare da cin zarafinsu har sau 123 a yankuna daban-daban na kasar.
Wanann mataki kuwa ya zo tun bayan abubuwan ad suka faru a birnin Paris na kai hari kan babban ofishin jaridar Charlie Hebdo, inda ake kai hari kan musulmi babu gaira babu sabar.
3209007