Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almujiz cewa, Ahmad Tayyib a wani jawabi da ya gabatar a wani taron kara wa juna sani a UAE ya bayyana cewa, bisa la’akari da rudani da aka shiga a wanna lokaci musulmi na bukatar yin nazari danagane da wasu abubuwan da aka rubuta a cikin addinin musulunci domin cire abubuwan da aka shigar da suke bata sunan wannan addini.
Malamin ya ci gaba da cewa akwai abubuwa da dama da a ka shigar da sua cikin addinin muslunci da bas u da alaka da muslunci, wasu a bangaren shari’a ko kuma ahukunce-hukunce da akida da sauransu, wanda hakan ne bababn makamin da yan ta’adda suka rike a cikin dukkanin ayyukansu na bata sunan muslunci a duniya.
Ahmad Tayyib ya kara da cewa dole ne sai an zauna an yi bitar dukkanin abubuwan da suka kamata, domin tace abin da yake bisa tafarki da kuma abubuwa na shirme da aka shigar, wadanda ake kallonsu a matsayin hukuncin addini, domin ta hka ne kawai a cewarsa za a gyara tunain masu tasowa daga cikin su zama kan tafarki da yafi dacewa da addininsu.
3228582