IQNA

An Kafa Wasu Allun Na Nuna Kyamar Musulunci A Tashar Metro A New York

23:51 - May 01, 2015
Lambar Labari: 3239040
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da kokarin dusashe hasken muslunci da kuma bata shi a idon duniya wasu masu tsakanin kiyayya da musulmi sun saka kalmomin batunci ga addinin muslunci a motoci da tashohin jirgin kasa.

Kamfanin dillancin labarn Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Turkish Weekly cewa, a ranar alhamis da ta gabata masu tsakanin kiyayya da musulmi a birnin New York sun saka kalmomin batunci ga addinin muslunci a motoci da tashohin jirgin kasa na birnin, suna masu nuna cewa asalin addinin muslunci ne ta’addanci.
Ana bayar da kariya ha masu aikata irin wannan mummunan aiki a kasar ne ta hanyar bayyana su a matsayin masu yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi, duk kuwa da cewa bayan da suka yi hakan hukumar kula da zirga-zirga ta birnin New ta kudiri aniyar fitar da kudirin cewa bas u da hakkin cin zarafin addinin muslunci.
Wanbnan dai bas hi ne karon farko da ake aikata irin wannan barna  akasar ta Amurka ba da sunan yancin fadar albarkacin baki, kuma masu yin hakan kungiyoyi ne na yahudawan sahyuniya, da kuma wasu kungiyoyin da suke da alaka da su, da suke taya su yin hakan.
Baya ga birnin New York a biranan Los Angles da Chicago d akuma Washington gami da Filadelfia duk an yi hakan, da suna yancin bayyana ra’ayi da fadar albarkacin aki.
3237929

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha