Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic-College cewa, wannan kwaleji na shirin shirin gudanar da wani taron kara wa juna sani kan mazhabar shi’a domin kara ilmantar da masu bincike kan hakan.
Bincike kan shi’anci da kuma dukkanin ilmomi da suka shafi wannan mazhaba na daga cikin abubuwan da jami’oin Amurka ta yamma ke mayar da hankali kansa wajen bincike, domin bayar da dama ga masu son fadada masaniyarsu kan wannan fage, da hakan ya hada ilmomin na kida da falsafa da sauransu.
Daga cikin abin da zaman taron karawa juna na kwalejin muslunc zai mayar da haknakali kansa har da matsayin Imam Hussain (AS) da kuma gudunmawar da ya bayar wajen kara bunkasa wannan makaranta da kuma bayar da darussa kyawawan darussa ga ‘yan adam
Manyan malaman jami’oi daga Birtaniya, Canada, Amurka, Danmark, Qatar da kuam Turkiya za su gabatar da jawabai a wurin wanann zaman taron.
Dr. Muhammad ali Shemali shi ne babban daraktan bangaren bincike kan ilmomin mulunci a wannan kwaleji, kuma shi ne ya dauki nauyin shirya wannan babban taron karawa juna sani.
3260619