IQNA

Sojojin Iraki Suna Samun Nasara Ne Kan Daesh Tare Da Taimakon Sojin Sa Kai

23:04 - May 08, 2015
Lambar Labari: 3274325
Bangaren kasa da kasa, sojojin kasar Iraki tare da taimakon dakarun sa kai da suka hada da na kabilun yan Sunnah suna ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan Daesh (ISIS) a cikin yankuna da daman a lardunan kasar.

 

Kamfanin dilalncin l;abaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-alam cewa, a zantawarsa da wannan kafa ta yada labarai a yammacin jiya, Hadi Al-Amiri kwamnadar rundunar sa kai ta badar ya bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a cikin makonni biyu zuwa uku da suka gabata, inda rundunar sojin Iraki tare da taimakon sojojin sa kai daga dukkanin bangarori na al'ummomin Iraki suke ci gaba fatattakar 'yan ta'addan Daesh.

A bangare guda kuma Hadi Amiri ya kore abin da ya kira farfagandar da wasu kafofin yada labarai suke yadawa, a kan cewa abin da ke faruwa a Iraki yaki ne tsakanin yan sunna da 'yan shi'a, inda ya ce dukkanin sojojin sa kai da suke taimaka ma rundunar sojin Iraki  da suka fito daga lardunan Salahudin da Anbar 'yan sunnah ne, domina cewarsa dan ta'adda bai bance dan sunna ko dan shi'a ko bakurde ko kirista, aikinsu shi ne kisan dan adam ba tare da rahma ba.

Ya ci gaba da cewa abin ban takaici yadda wasu daga cikin kasashen yammacin trai ke ta hankoron ganin sun mayar da aiki baya a Irakia yakin da ake yi da ‘yan ta’adda Daesh, alhali kuwa babu wanda bai san cewa hadarin wadannan mutane bai takaita da kasar ba kawai, abu ne da ke shafar kowa  ahalin yanzua  duniya, amma kuma ana ta kokarin danganta kokarin sojojin sa kai da batu na bangaranci wand aba gaskiya ba ne.

Dangane da irin rawar da kabilun larabawan sunan suke takawa wajen yaki da wannan kungiyar ta ta’addanci kuwa, y ace da ba domin taimakon da kabilun suka bayar ba, da sauran masu bayar da dauki na sa kai, da ba a samu irin wannan gagarumar nasara kan yan ta’addan ba.

 

3273268

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha