Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran sabanet cewa, malaman addinin muslunci Yemen sun tuhumi masarautar saudiyya da keta dukaknin hurumi na dokoki da kaidoji na kasa da kasa harin da take kaddamarwa kan al’ummar kasar babu kakakutawa.
Babban sakataren kungiyar Ummah ta kasar Yeman ya bayyana cewar manufar kasar Saudiyya ta kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yeman ita ce kokarin hana al’ummar Yeman ‘yantar da kansu daga kangin siyasarta ta babakere kan kasar ta Yeman.
Sakataren kungiyar Ummah ta kasar Yeman ya bayyana cewar Mahukuntan Saudiyya sun dauki matakin kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yeman ce sakamakon ganin al’ummar kasar sun yunkuro domin kawo karshen bakar siyasarsu ta babakere kan kasar musamman kakkabe hannun ‘yan koransu da suke rike da madafun iko a kasar ta Yeman.
Ya kara da cewar mahukuntan Saudiyya suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yeman tare da rusa duk wani abu mai amfani a kasar da nufin ganin al’ummar Yeman sun ci gaba da kasancewa cikin bakin talauci da bukatuwa zuwa gare su, don su samu damar juya akalar siyasar kasar yadda suke so a nan gaba.
Hatta kungiyar kare hakkokin mata da kanan yara ta UNICEF ta zargi masarautar ta Saudiyya da yin kisan gilla kan kanan yara babu daira babu sabar a harin wuce gona da iri da take kaiwa a kasar.