IQNA

Wani Malamin Saudiyya Ya Yi Kira Zuwa Ga Tawaye Da Shi’a

23:47 - May 16, 2015
Lambar Labari: 3304140
Bangaren kasa da kasa, Salman Audah wani fitaccen malamin wahabiyan Saudiyya ya bayyana cewa mabiya mazhabar shi’a a tarihinsu sun yi cin fuska ga sahabbai saboda haka yana kiran matasan shi’a da su yi wa wannan akidar tawaye.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Al-youm cewa, a ci gaba da samun wahabiya masu tsananin kiyayay da tafarkin iyakan gidan  manzo, wani bawahabiyen ya fito ya sheda cewa mabiya mazhabar shi’a a cikin tarihinsu sun yi ci mutuncin sahabban manzon (SAW) saboda haka yana kiran matasan shi’a da su tashi tsaye su yi wa wannan akidar tasu tawaye domin babu makoma mai kyau a cikinta  acewarsa.

Wannan mutm yana daya daga cikin wahabaiya masu tsananin kiyayya da shi’a a kasar ta saudiyya, wadda ta ginu a kan kirkiro karairayi domin yin batunci ga mazhabar iyalan gidan amnzon Allah, wanda kuma dam aba sabon lamari ba ne idan aka yi la’akari da tushen wahabiyanci, ya samo asali ne da akidar kin tafarkin amnzon Allah amma da sunan bin sunnar amnazon Allah.

A ci gaba da soki borotsonsa, malamin wahabiyan ya ce akwai lokaci mai zuwa da asalin shi’a zai kare bisa ga irin bincike da ya yi, kuma yaynsu masu tasowa za su yi musu yawaye su yi watsi da wannan akida, su kama akidar sunna da suke rayawa.

3304052

Abubuwan Da Ya Shafa: wahabiyanci
captcha