IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allawadai Da Gina Matsunnan Da Isra’ila ke Yi

23:53 - May 16, 2015
Lambar Labari: 3304142
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta sake yin Allawadai da ci gaba da gina matsigunnan yahudawa da Isra’la ke yi a yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar faransa cewa, kakakin bababn sakataren majalisar dinkin duniya Ban ki Moon ya bayyana cewa, a bin da Isra’ila take yin a ci gaba da gina matsigunnan yahudawa da Isra’la ke yi a yankunan gabar yamma da kogin Jordan ya sabawa dukaknin dokoki na kasa da kasa, kuma yana yin Allawadai da hakan.

 

Ban Ki Moon ya jadda kiransa ga haramtacciyar kasar Isra’ila da ta gagaguta kawo karshen gina matsugunnan yahudawan da take a  cikin a yankunan palastinawa, matukar dai abin da take fada na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakaninta da palastinawa da gaske ne.

Rahoton y ace gidanma sabbin matsugunnai da Isra’’ila ke shirin yi a yankin, bayan da majalia ta maince da gina matsugunnai 85, hakan ya yi hannun riga da shirin zaman lafiya baki daya.

 

3304054

Abubuwan Da Ya Shafa: UN
captcha