IQNA

An fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa Baki daya a Kasar Aljeriya

23:58 - June 02, 2015
Lambar Labari: 3310741
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar ku'ani mai tsarki ta kasa baki daya akasar Aljeriya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habart cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Al-shuruq Online cewa, an fara gudanar da gasar ne kamar yadda aka saba a kowace shekara a tsakanin shekaru 20 zuwa 25, wanda hakan ke bayar da dama share fage na zabar wadanda ke wakiltar kasar a gasa ta duniya.

Bayanin ya ci da cewa a wannan gasa za a fitar da mutane 10 daga cikin masu karawa da juna, wanda kuma wadannan mutane 10 n za su wakilci a kasar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsa kasa da kasa ake gudanarwa a cikin watan Ramadan mai alfarma.

Kasar dai na daga cikin kasashen da suke bayar da muhimamnci matuka wajen yada koyarwa ta kur'ani mai sarki ta hnayr makarantu na cikin gida musamman ma makarantun addini, wadanda daga bisani kuma sukan fitar da makaranta da suke samun shahara a duniya.

Tsarin karatun kasar ta Aljeriya dai yay i kama da tsohon tsari da ake bi a kasashen yankin, wanda kafin yaro ya kai wata marhala ta shekaru ya kamala hardace kur'ani mai tsarki tare da ilmin kyautata karatun, daga bisani kuma yakan wuce har zuwa jami'a, a ranar 27 na Ramaan za a girmama wadanda suka nuna wazo.

Wannan gasa dai ta kur'ani da Tajwidi ta Aljeriya Muhammad Isa ministan kula da harkokin addini na kasar ne da kansa ke jagorantarta.

3310432

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeria
captcha