IQNA

Bikin Saka Kyandura A Daren Sha Biyar Na Sha'aban A Binin Karbala

23:44 - June 04, 2015
Lambar Labari: 3310923
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da bikin saka kyadura da aka saba yi a kowace shkara a birnin Karbala domin tunawa da ranar haihuwar Imam Hujja (AJ)


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a jiya an gudanar da bikin saka kyadura a birnin Karbala mai tsarki domin tunawa da ranar haihuwar Imam Zaman (AJ) da ake yi a kowace shekara.

Bayanin ya ci gaba da cewa an saka wadannan kyandura a daidai daren na sha biyar ga wanann wata mai alfarma, domin girmama matsayin daren wanda a cikinsa aka haifi limamin zamani Imam Mahdi (AJ) inda aka saka kyandura 1181 aka kawata wurin da su a matsayin adadin shekarun wannan babban bawan Allah da duniya ke jira domin tseratar da ita da umarnin ubangiji.

An fara gudanar da wannan biki ne tun shekaru 15 da suka gabata, wato shekaru biyu kafin kifar da gwamnatin zalunci da dannin ta tsohon shugaban kasar ta Iraki.

Abbas A-musawi shi ne shugaban bangarn da ke jagorantar gudanar da wannan aiki mai albarka, ya bayyana cewa sun fara yin hakan ne tun a cikin shekara ta 2001, duk kuwa da barazanar da suke fuskanta  a lokacin daga shugaban kasar mai mulkin zalunci.

Taron na Karbala a jiya a ya samu halartar dubun dubatar muminai daga sassa daban-daban na kasar da kuma wajenta, domin raya wannan dare mai albarka a birnin Kalbala mai tsarki, wanda a cikinsa ne hubbaren kakan Imam yake amincin Allah ya tabbata a gare su.

3310766

Abubuwan Da Ya Shafa: karbala
captcha