Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na hqmi.orgcewa, an kammala wanann taron gasar kur’ani da aka gudanar a garin Al-qabah na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann gasa ta hada bangarori na harda a izihi na 20, da kuma na 15, sai kuma 10, sai kuma 8 da kuma 5, hakan yana daga cikin tsarin da aka yi tun daga farko, ta yadda kowane bangare na daga cikin mahardatan da kuma makarantan zai samu shiga.
Kasr Tunisia na daga cikin kasashen nahiyar ad suke mayar da hankali wajen bunkasa lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki, ta hanyar koyarwa a makarantu, da kuma shirya gasa irin wanann domin kara kwadaitar da jama’a musamamn ma matasa daga cikinsu.
Gasar dai ta samu karbuwa daga bangarori daban-daban na al’umma, kuma hakan ya kara zaburar da matasa da dama wajn mayar da hankali ga lamrin kur’ani mai tsarki, ta fukar karatu da kuma harda, da koyon ilimin kyautata karatun.
3311312