Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na AFP cewa, Muhammad Kharaki shugaban cibiyar muuslmi mazauna kasar Sweeden ya bayyana cewa, sun samu damar fitar da wani bayani domin sawaka wa wadanda suke zaune a yankunan da ran aba ta faduwa a cikin kasar dangane da azumin watan Ramadan bisa la’akari da matsalolin da suke fuskanta.
Y ace wanann zai taimaka matuka, domin kuwa a cewarsa a birnin Stockholm suna ganin faduwar rana lokaci zuwa lokci, amma a wasu biranan kamar Crona ba su ganin faduwar a lokacin sam, saboda haka a kwai matsala a wurin azumi a cikin irin wadannan yankuna.
Y ace bisa ga irin fatawar da malamai suka fitar bayan yin dubi da nazari mai zurfi kan wanann batu, an fitar da fatawa ga dukaknin musumi da suke rayuwa a yankunan da ran aba ta faduwa kan cewa ba za su yi azumi ba, har sai lokacin da rana take faduwa sai rama a zumin.
Wannan matsala dai ta jima tana ci wa musulmi mazauna wadannan yankuna tuwo a kwarya, amma dai a wanann karon samu sauki ta hanyar wanann fatawa ta malamai.
Yanzu haka dai a kasar Sweden akwai musulmi kimanin dubu 350 daga cikin mutanen kasar da suka yawan miliyan tara baki daya.
3313309