IQNA

Musulmi Da Kiristoci Sun Gudanar Da Zama A Amurka Domin Kara Samun Fahimtar Juna

23:58 - June 14, 2015
Lambar Labari: 3314380
Bangaren kasa da kasa, wasu malamai 14 daga cikin mabiya addinin muslunci da kuma 11 na mabiya addinin kirista akasar Amurka sun gdanar da wani zama domin kara samun fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Kamfanin dllancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Umar Bavar Sharlut daya daga cikinwakilan addinin muslunci a Amurka ya bayyana cewa malamai daga cikin mabiya addinin muslunci da kuma na mabiya addinin kirista  akasar Amurka sun gdanar da wani zama domin kara samun fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin bangarorin wadanda kan fuskanci matsaloli na rashin fahimta.

 

Ya ci gaba da cewa hakika na samu a bin da ake bukata  awannan zama, domin dukkanin bangarorin biyu sun gamsu da bayan kowane bangare, kuma yana ganin daga wannan lokacin za a samu canji matuka dangane da matsayin wasu mabiya addinin kirista dangane da addinin.

Dangane da dalilin da yasa yake ganin za a samu wannan canji kuwa, har yadda zaman ya kasance ya kunshi malamai daga dukkanin bangarorin, wadfanda suke da fada a ji kan miliyoyin mabiyansu, musamman ma dais u mabiya addinin kirista wadanda sun fi yawa.

 

Wanann zama dai ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli na karuwar kymar addinin muslunci da kuma mabiyansa a cikin kasar ta Amurka, wanda kuma hakan lamari ne mai matukar hadari ga makomar kasar.

3313825

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha