Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almusalla cewa, Nuri Maliki mataimakin shugaban kasar Iraki ya bayyana cewa, hakika fatawar da manyan malaman kasa suka bayar domin yaki da yan ta’adda masu kafirta musulmi, ta yi bababn tasiri a dkkanin nasarorin da ake samu a kansu.
A bangare guda kuma rahotanni sun ce dakarun tsaron kasar Iraki sun hallaka ‘yan ta’adda kimanin arbain a yammacin kasar A wata sanarwa da Ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, ta ce a wannan talata dakarun tsaro hadin gwiwa sun gano maboyar ‘yan ta’adda kimanin sha biyar a gariruwan Alkarama, fuhailat dake garin Ramadi na jahar nbar dake yammacin kasar, inda suka hallaka ‘yan ta’adda da kuma lalata motocin guda daga ciki har wata mota shake da bama-bamai.
A bangare kakakin shugaban kasar Iraki Khalid Shawani ya sanar da kotua ayanke hukuncin kisa kan wasu Mutane dari saboda da laifukan ta’addanci a kasar, daga shekara ta 2006 zuwa yanzu ‘yan ta’adda dari shida aka zartawa hukuncin kisa a kasar.
Shugaban kasar ta Iraki ya ce kadda a yi jinkiri wajen zartar da hukuncin matukar aka tabbatar da laifin su.