Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Iraq Net cewa, Sheikh Khalid Mulla shugaban kwamitin malaman snnah a Iraki ya bayyana cewa hudubobin da wasu yan sunna ke yin a tunzura jama’a zuwa ga ta’addanci ba su dace da sunna ko kuma koyarwar manzo ba.
A bangare guda kuma rahotanni na cewa sojojin kasar Iraki da suke samun daukin dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kwato garuruwa guda bakwai a lardin bar na kasar daga hannun ‘yan ta’adda.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Irakin sun bayyana cewar a hare-haren da sojoji da dakarun sa kai din suka kai wa ‘yan ta’adda a garin Karma da ke tsakiyar kasar, sun sami nasarar hallaka wasu ‘yan kungiyar ta Da’esh da dama cikinsu kuwa har da wasu kwamandojin soji su bakwai.
Tun a ranar Litinin din da ta gabata ce sojojin na Iraki tare da dakarun sa kan suka fara kaddamar da hare-harensu inda suka kwato kauyuka da daman a gundumar ta Karma kamar yadda kuma suka sami nasarar fatattakan ‘yan kungiyar da suka sake dawowa da nufin kwato wasu daga cikin wadannan garuruwan.
Ita dai gundumar ta Karma ta kasance mai muhimmancin gaske ga dukkanin bangarorin biyu ganin cewa garin yana daga cikin garuruwan da ‘yan ta’addan suke amfani da shi wajen isar da bama-bamai zuwa birnin Bagadaza, babban birnin kasar Irakin.