IQNA

Jamusawa Sun Yi Jerin Gwanon La’antar Masu Kiyayya da Muslunci A Frankfort

23:32 - June 23, 2015
Lambar Labari: 3317965
Bangaren kasa da kasa, Bayan taron da masu kiyayya da muslunci suka yi su kamar 200 fiye da Jamusawa 2000 ne suka yi jerin gwano a birnin Frankfort, domin nuna adawarsu ga kungiyar nan mai kiyayya da musulmi ta PEGIDA.


Kamfanin dillancin labaran Inqa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, kimanin jamusawa 2000 ne suka yi jerin gwano a birnin Frankfort domin nuna adawarsu ga kungiyar nan mai tsananin gaba da musulmi ta PEGIDA suna la’atar kungiyar da kuma ayyukan da take yin a nem,an tashin hankali da tsokana.

A ranar Asabar da ta gabata ce kimanin mutane 200 daga cikin magoya bayan kungiyar ta PEGIDA ska gudanar da gangami a dandalin Rossmarkt da ke cikin birnin, suna masu nuna kin jinnin addinin muslunci da musulmi kamar dai yadda suka saba yi a sassa daban-daban na kasar.

Zanga-zangar ta jiya dai ta hada da kungiyoyin farar hula da kma wasu daga cikin yan siyasar kasar wadanda bas u amince da irin wannan salon a nuna kiyayya ga wani bangaren al’ummar kasar saboda addininsu ko wata akida tasu ba, wanda hakan ke nni da cewa al’ummar Jamus bas u amince da munan akidu na kungiyar ba.

Tuna  cikin shekara ta 2014 ce aka kafa wannan mummunar kungiyar da take dauke muggan akidu na kin muslunci, tun bayan lokacin kuma ta yi ta gudanar da jerin gwano a lokutan da dama  akasar har ma da wasu kasashen daga cikin kashen nahiyar turai.

A duk lokacin da ta yi hakan, a bangare guda kuma ta kan fuskanci wata zanga-zangar kiyayya da adawa da ita da kuma manufofinta a cikin jamus da ma sauran kasashen nahiyar turai.

3317334

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha