Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, wasu daga cikin mabiya addinin muslunci da suke yankin ne suka dauki nauyin gudanar da wannan buda baki ga dukkanin mutanen da ake gayyata a kowace rana.
Masallacin na Darul Asrar yana bayar da buda baki ga dubban mutane a cikin watan Ramadan mai alfarma idan aka yi la’alari da adadin mutanen da yake baiwa buda bakia kowace a lokacin shan ruwa, daga cikin mutanen da ake gayyata kuma akwai musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Muhamamd Ahmad shi ne shgaban bangaren kula da ayyukan masallacin ya bayyana cewa, babban abin da wanann aiki ko koyarwa dsa kuma sakon da yake isarwa shi ne, adddinin muslunci na zaman lafiya ne tare da sauran addinai, kuma yana girmama kowa da son ganin al’umma ta fahimci juna duk kuwa da banbancin addini ko akida ko fahimta a tsakaninsu.
Ya kara da cewa ta wanann hanya za su iya samun damar hada mutane daban-daban da suke da addinai mabanbatna da kuma akidu a wuri guda, su ci abinci su tattauna su kara fahimtar juna, ta yadda za su zauna lafiya da jna, baya ga haka kuma suna koyar da mutane taimako kamar yadda addinin musulunci ya koyar.
3317359